unfoldingWord 42 - Yesu ya Koma Sama
Outline: Matthew 28:16-20; Mark 16:12-20; Luke 24:13-53; John 20:19-23; Acts 1:1-11
Script Number: 1242
Language: Hausa
Audience: General
Genre: Bible Stories & Teac
Purpose: Evangelism; Teaching
Bible Quotation: Paraphrase
Status: Approved
Scripts are basic guidelines for translation and recording into other languages. They should be adapted as necessary to make them understandable and relevant for each different culture and language. Some terms and concepts used may need more explanation or even be replaced or omitted completely.
Script Text
A ranar da aka tashi Yesu daga matattu, biyu daga cikin almajiransa na tafiya zuwa wani gari dake kusa. Da suna tafiya, suna magana akan abinda ya faru da Yesu. Sun sa bege cewa shine Almasihu, amma kuma an kashe shi. Yanzu mata sun ce yana da rai kuma. Ba su san abinda zasu gaskanta ba.
Yesu ya zo wurin su, ya fara tafiya da su, amma ba su gane shi ba. Ya tambaye su maganar me suke yi, sai suka gaya masa dukkan manyan abuauwan da suka faru game da Yesu, a 'yan kwanaki da suka wuce. A tunanin su, suna magana ne da wani bako wanda bai san abin da ya faru a Urushalima ba.
Sa'annan Yesu ya bayyana masu abinda maganar Allah ya fadi game da Almasihu. Ya tunashe su cewa annabawa sun ce Almasihun zai sha wahala, a kuma kashe shi, amma zai tashi kuma a rana ta uku. Da suka isa garin da mutanen nan biyu suka yi shirin sauka, yammaci ya kusa.
Mutanen nan biyu su ka gayyaci Yesu ya zauna tare da su, sai ya amince. Sa'anda suka shirya domin cin abincin maraice, Yesu ya dauki curin gurasa, ya gode wa Allah domin ta, ya kuma karya ta. Nandanan, suka gane cewa Yesu ne. A wannan lokaci kuwa, Yesu ya bace daga ganin su.
Sai mutanen biyu suka ce wa juna, "Ai Yesu ne! Shi yasa zuciyar mu take kuna lokacin da ya ke fassara mana maganar Allah!" Nandanan, suka koma Urushalima. Da suka iso, suka fada wa almajiran, "Yesu yana da rai! Mun gan shi!''
Yayin da Almajiran suna cikin magana, nandanan Yesu ya bayyana a cikin dakin tare dasu, sai ya ce, "Salama a gareku!" Almajiran suka yi zaton shi fatalwa ne, amma Yesu yace masu, "Donme kuke jin tsoro kuna kuma shakka? Ku dubi hannaye na da sawaye na. Fatalwa bashi da jiki kamar yadda nake dashi." Domin tabbatar masu shi ba fatalwa ba ne, sai ya roke su wani abu ya ci. Suka ba shi gutsuren dafaffen kifi, sai ya ci.
Yesu ya ce, "Na gaya maku cewa, dukkan abubuwan da aka rubuta game da ni a maganar Allah dole za'a cika su." Sai ya bude fahimtar su domin su iya gane maganar Allah. Ya ce, "A rubuce yake da dadewa cewa Almasihu zai sha wahala, ya mutu, ya kuma tashi daga matattu a rana ta uku."
"An kuma rubuta cikin nassi cewa almajirai na zasu yi shela kowa ya tuba domin ya karbi gafaran zunuban sa. Zasu yi haka da fari cikin Urushalima, sa'annan suje ga dukkan kabilun mutane ko ina. Ku shaidu ne na wadannan abubuwa."
A cikin kwanaki arba'in na gaba, Yesu ya bayyana ga almajiran sa sau dayawa. Wani lokaci ma har ya bayyana ga mutane fiye da 500 lokaci guda! Ya tabbatar wa Almajiransa ta hanyoyi da dama, cewa yana da rai, ya kuma koyar dasu game da mulkin Allah.
Yesu ya ce wa Almajiransa, "An bani dukkan iko a sama da kuma kasa. Saboda haka ku je, ku Almajirantar da dukkan kabilun mutane, ta wurin yi masu baftisma, acikin sunan Uba, da na 'Da, dana Ruhu Mai Tsarki, kuma ta wurin koyar da su, su yi biyayya da dukkan umarnin da Na baku. Ku tuna, Zan kasance da ku kullayomin."
Bayan kwanaki arba'in da tashin Yesu daga matattu, ya ce wa almajiran sa, "Ku zauna a Urushalima har sai Ubana ya ba ku iko, sa'anda Ruhu Mai Tsarki zai sauko a kan ku." Sai Yesu ya tafi sama, sa'annan wani gajimare ya rufe shi daga idanun su. Yesu ya zauna a hannun dama na Allah ya kuma yi mulki bisa dukkan abubuwa.