unfoldingWord 01 - Halitta
Outline: Genesis 1-2
Script Number: 1201
Language: Hausa
Theme: Bible timeline (Creation)
Audience: General
Genre: Bible Stories & Teac
Purpose: Evangelism; Teaching
Bible Quotation: Paraphrase
Status: Approved
Scripts are basic guidelines for translation and recording into other languages. They should be adapted as necessary to make them understandable and relevant for each different culture and language. Some terms and concepts used may need more explanation or even be replaced or omitted completely.
Script Text
Ga yadda abubuwa duka suka kasance, tun daga farko. Allah ya hallaci sammai da dukan abubuwan da ke cikin su chikin kwana shida. Bayan Allah ya hallaci duniya, duhu ya maimaye ta, cikinta kuma wofi ne, ba a kuwa hallici kome ba. Amma Ruhun Allah yana nan bisa ruwa.
Sa'annan Allah ya ce, "Bari haske ya kasance!" Sai haske ya kasance. Allah ya ga hasken yana da kyau, ya kira shi "yini". Ya raba shi daga duhu wanda ya kira "dare." Allah ya hallaci haske a rana ta fari na halitta.
A rana ta biyu ta halitta, Allah ya yi magana ya hallici sarari bisa duniya. Ya yi sarari ta wurin raba ruwan sama daga ruwan kasa.
A rana ta ukum Allah ya yi magana ya raba ruwa daga busasshiyar kasa. Ya kira busasshiyar kasar "duniya," ya kuma kira ruwan, "tekuna." Allah ya ga abinda ya halitta yana da kyau.
Sa'annan Allah ya ce, "Bari kasa ta fitar da itatuwa iri iri da tsire tsire." Haka kuma ya faru. Allah ya ga abinda ya halitta yana da kyau.
A rana ta hudu na halitta, Allah ya yi magana, ya yi rana da wata da kuma taurari. Allah ya sa su, su ba da haske bisa duniya, su kuma raba yini da dare, lokatai da shekaru. Allah ya ga abinda ya halitta yana da kyau.
A rana ta biyar, Allah ya yi magana, ya yi dukkan abubuwan dake fitto a ruwa da dukkan tsuntsaye. Allah ya ga yana da kyau, ya kuma albarkace su.
A rana ta shida na halitta, Allah ya ce, "Bari kowanne irin dabbobin kasa su kasance!'' Sai ya faru kamar yadda Allah ya fada. Wadansu dabbobin gida ne, wadansu kuma masu rarrafe ne a kasa, wadansu kuwa dabbobin jeji ne. Sai Allah ya ga yana da kyau.
Sa'annan Allah ya ce, "Bari mu yi mutane cikin surarmu, su zama kamarmu. Za su zama da iko bisa duniya da dukan dabbobi."
Sai Allah ya dibi kasa, ya siffanta shi mutum, ya kuma hura rai a cikinsa. Sunan mutumin nan Adamu ne. Allah ya dasa gona inda Adamu zai iya zama, ya ajiye shi a wurin ya lura da ita.
A tsakiyar gonar, Allah ya dasa itatuwa biyu na musamman- itacen rai da itacen sanin nagarta da mugunta. Allah ya gaya wa Adamu zai iya ci daga kowanne itace da ke gonar, amma banda itacen sanin nagarta da mugunta. Idan ya ci daga wannan itacen, zai mutu.
Sa'annan Allah ya ce, "Bai kyautu mutum ya kasance shi kadai ba." Amma babu ko daya daga cikin dabbobin da zai iya zama mataimakin Adamu.
Sai Allah ya sa Adamu ya yi barci mai zuryi. Sa'annan Allah ya dauki daya daga cikin hakarkarin Adamu ya maida shi mace ya kawo masa ita.
Da Adamu ya ganta, ya ce, "Hakika! Wannan ta yi kama da ni! Bari a kirata 'Mace,' domin an yi ta daga Namiji." Shi yasa namiji ke barin mahaifinsa da mahaifiyarsa ya zama daya da matarsa.
Allah ya yi namiji da ta mace cikin surarsa. Ya albarkacesu ya ce masu, "Ku haifi 'ya'ya da yawa da jikoki ku cika duniya!" Allah ya ga dukan abubuwan da ya yi suna da kyau kwarai, ya kuma gamsu da dukansu. Duk wannan ya faru a rana ta shida na halitta.
A rana ta bakwai, Allah ya gama aikinsa. Sai Allah ya huta daga dukkan abinda yake yi. Ya albarkaci rana ta bakwai, ya kebeta da tsarki, domin a ranar ne, ya huta daga aikinsa. Haka Allah ya hallici duniya da sammai da dukkan abubuwan dake cikinsu.