unfoldingWord 31 - Yesu ya yi Tafiya a kan Ruwa
Outline: Matthew 14:22-33; Mark 6:45-52; John 6:16-21
Script Number: 1231
Language: Hausa
Audience: General
Genre: Bible Stories & Teac
Purpose: Evangelism; Teaching
Bible Quotation: Paraphrase
Status: Approved
Scripts are basic guidelines for translation and recording into other languages. They should be adapted as necessary to make them understandable and relevant for each different culture and language. Some terms and concepts used may need more explanation or even be replaced or omitted completely.
Script Text
Sa'annan Yesu ya fada wa almajiransa su shiga jirgin ruwa su haye zuwa wancan gefen tafki sa'adda da ya tsaya ya sallami taron. Bayan Yesu ya sallami taron, sai ya haura gefen tsauni domin ya yi addu'a. Yesu na wurin nan shi kadai, ya kuma yi addu'a har zuwa kurewar dare.
A wannan lokaci, almajiran na tukin jirgin ruwansu, amma a kurewar daren, sun kai tsakiyar ruwan ne kawai. Suna tuki da wahala, domin iska na hurawa da karfi gaba da su sosai.
Sa'annan Yesu ya gama addu'a sai ya tafi wurin almajiran. Yayi tafiya akan ruwa yana haye tafkin zuwa wurin jirgin su!
Almajiran suka tsorata kwarai da suka ga Yesu, domin a tunaninsu fatalwa suke gani. Yesu ya san cewa tasorace suke, sai ya kira su, ya ce, "Kada ku ji tsoro. Ni ne!"
Sai Bitrus ya ce wa Yesu, "Ya shugaba, idan dai kai ne, ka umarce ni in zo wurin ka a kan ruwan." Yesu ya ce wa Bitrus, "Zo!"
Sai Bitrus ya fita daga jirgin ruwar ya fara tafiya zuwa wurin Yesu a kan ruwa. Amma da yayi tafiya kadan, sai ya kau da idanunsa daga Yesu ya fara duban rakuman ruwa, yana jin yadda kakkarfar iskar take.
Sai Bitrus ya ji tsoro ya kuma fara nutsewa a ruwa. Sai yayi kuka, "Ya shugaba, ka cece ni!" Nandanan Yesu ya isa wurin sa ya kama shi. Sa'annan ya ce wa Bitrus, "Kai mutum mai karamin bangaskiya, me ya sa ka yi shakka?"
A lokacin da Bitrus da Yesu suka shiga jirgin ruwan, nan da nan iskar ta dena kadawa, ruwan kuma ya natsu. Almajiran suka yi mamaki. Suka yi wa Yesu sujada, suna cewa, "Gaskiya, kai Dan Allah ne."